NYT: Boko Haram su na amfani da jiragen yaki maras matuki wajen kai hari

NYT: Boko Haram su na amfani da jiragen yaki maras matuki wajen kai hari

Babbar Jaridar Amurkar nan wanda ta shahara Duniya New York Times, ta bada rahoto cewa sojojin Najeriya sun rasa karsashi wajen yaki da ‘yan ta’ddan Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Rahotannin jaridar sun bayyana cewa akwai cin karo tsakanin abin da gwamnatin Najeriya da jami’ai su ke ikirari na cewa an ga bayan ‘yan ta’dan Boko Haram da ainihin abin da ke faruwa.

Jaridar kasar wajen ta bayyana cewa ‘yan Boko Haram su na aiki ne da manyan na’urori da makamai na zamani yayin da Dakarun Sojojin Najeriya ke amfani da tsofaffin kayan aiki da salo.

Fiye da shekaru goma kenan ana fama da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin kasar da kewayen Afrika. A baya gwamnati ta fito ta na cewa ta ci karfin ‘yan ta’ddan saura kuma diddigensu kurum.

Binciken da NY Times ta yi a Najeriya, ya nuna cewa sojojin Najeriya su na cikin wani hali na dar-dar da kokarin kare kan su a madadin a ce su ne su ke kai wa ‘yan ta’addan hari a inda su ke.

KU KARANTA: Buhari ya yi kira ga shugabannin Afrika su dage wajen yakar ta’addanci

Wasu Sojojin sun shafe shekaru uku su na fagen daga ba tare da sun koma gida ba. A sanadiyyar haka, makamai da motoci da sauran kayan aikin da ke hannun su, duk sun gaji inji rahoton.

A daidai wannan lokaci, ‘yan Boko Haram su na yawo a gari su na cigaba da ta’adi. Abin tada hankalin shi ne yanzu ‘yan ta’ddan su na aiki da jirgin da bai da matuki wanda ake kira ‘Drone.’

Irin wadanan jirage da ‘yan ta’ddan su ke amfani da su wajen shirya farmaki sun sha gaban wadanda ke hannun Sojoji inji Masana. A baya gwamna Umara Zulum ya taba fadin irin haka.

NY Times ta yi hira da mutanen Gari da Sojoji inda wasu su ka tabbatar masu da cewa sojoji na tserewa daga filin yaki saboda tsoron ‘yan ta’adda. Wasu Sojojin sun karyata wadannan labarai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel