Shugaba Buhari ya yi magana game da barazanar ‘Yan ta’adda a Duniya

Shugaba Buhari ya yi magana game da barazanar ‘Yan ta’adda a Duniya

Labarin da mu ke samu shi ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin kasashen Afrika wajen taron ECOWAS da su tashi tsaye wajen yaki da ta’addanci a Nahiyar.

Shugaban kasar ya nemi Takwarorinsa shugabanni su dage wajen ganin ‘yan ta’adda ba su rikita yankin Afrika ba. Shugaban na Najeriya yace dole ayi kokari wajen ganin jama’a sun zauna lafiya cikin aminci.

Buhari ya yi wannan kira ne a jawabinsa wajen babban taron ECOWAS na kasashen Afrika ta Yamma da aka shirya domin ganin gwamnatoci da shugabanni sun ga karshen ta’addanci da ya addabi jama'a.

Shugabannnin kasashe irinsu Chad da Mauritania sun halarci wannan taro na kwana guda inda Buhari ya ja masu kunnen cewa ‘yan ta’adda su na neman zama barazana a Afrika da ma fadin Duniya.

KU KARANTA: Gwamnonin Jihohi sun samu sabani da Jami’an Sojoji kan kudin tsaro

“Don haka ya zama nauyi a kan mu, mu dage wajen ganin mun yi nasara a yaki da ‘yan ta’adda. Dole mu fatattaki wadannan bara-gurbi da Yankin mu.” Inji Shugaba Buhari a wajen taron na jiya.

A jawabinsa, Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa yawan hare-haren da ‘yan ta’adda su ke kai wa, da kuma irin manyan makaman da su ke samu, abin tada hankali ne ga al’ummar Afrika.

Bugu da kari, shugaban kasar ya nuna cewa ana samun alaka tsakanin ta’addanci da ta’adin yau da kullum, wanda ya nuna cewa hakan abin damuwa ne don haka ya yi kira da a zage dantse.

A wajen wannnan taro da aka shirya Ranar Asabar, 14 ga Watan Satumba, 2019, a babban birnin Ouagadougou da ke kasar Burkina Faso, Buhari ya yi magana kan yakinsa da Boko Haram.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel