Gwamnatin jihar Yobe ta karbe wani filinta mai girman hekta 3.5 daga hannun rundunar soji

Gwamnatin jihar Yobe ta karbe wani filinta mai girman hekta 3.5 daga hannun rundunar soji

Gwamnatin jihar Yobe ta karbo daya daga cikin kadarorinta, fili mi girman hekta 3.8, daga hannun rundunar soji a Kaduna.

Da yake mika filin ga wakilin gwamnatin jihar Yobe, kwamandan rundunar soji ta daya, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya bayyana cewa an warware badakalar batun filin ne sakamakon saka bakin da shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya yi.

Ya kara da bayyana cewa rundunar soji ta mika filin ga gwamnatin jihar ne saboda dalilan zaman lafiya da kuma girmama alakar da ke tsakaninsu.

A cewarsa, mika filin a hukumance zai bawa gwamnatin jihar Yobe damar yin amfani da wurin domin gina duk abinda take so.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda masu nasaba da IS sun kashe sojojin Najeriya 9, 27 sun bata

Da yake sa hannu a kan takardun karbar filin amadadin gwamnatin Yobe, sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, ya ce an warware batun takaddama a kan fili ne saboda kyakyawar alaka da girmama juna da ke tsakanin rundunar soji da gwamnatin jihar Yobe.

"Mu na masu farinciki a kan yadda aka warware matsalar cikin ruwan sanyi da girmama juna. Mun yi alkawari za mu yi amfani da filin wajen gina wani abu da zai taimaki mutanen jihar Yobe da ma kasa baki daya," a cewar Wali yayin da ya ke gabatar da jawabi.

Wali ya bayyana cewa nan bada dade wa ba gwamnatin jihar Yobe za ta fara aikin kewaye filin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel