Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane shida a Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane shida a Kaduna

A kalla mutane 10 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon sabon harin da aka kai a kauyan Fadaman Rimi a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

The Nation ta ruwaito cewa maharan sun kai harin ne a safiyar ranar Asabar inda suka iso garin dauke da bindigu kuma suka fara harbe-harbe.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu ya ce yana kan tattara bayanai saboda haka bai tabbatar da adadin wadanda aka ce sun mutu ba yayin hada wannan rahoton.

Kakakin 'yan sandan ya ce zai fitar da sanarwa da zarar ya kammala tattara bayanai kamar yadda majiyar ta Legit.ng ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

Wani wanda abin ya faru a gabansa ya ce maharan sun kashe mutane shida yayin da wasu da dama sun jikkata ciki har da wadanda harsashi ya raunata su.

A cerwar majiyar, "maharan sun iso kauyen mu mislain karfe shida na safe kuma suka kashe mutum shida cikin 'yan garin mu sannan suka sace masa kayayaki da shanu. Lokacin da suka iso muna cikin gida sai suka fara harbin duk wanda suka gani.

"Allah ne kawai ya tsiratar da mu domin lokacin da mutane ke kokarin tserewa, maharan suna ta harbin mu. Lamarin babu dadi ko kadan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel