Gangar danyan man fetur ya kara kudi bayan OPEC ta ki rage buri

Gangar danyan man fetur ya kara kudi bayan OPEC ta ki rage buri

Mun samu labari cewa man Kasar Amurka ya kara daraja inda ya karu da akalla kashi 2% a cikin makon nan. A daidai wannan lokaci kuma danyan man Najeriya ya dada yin kudi a kawuwa.

A cewar jaridun kasar waje, man Najeriyan ya dada kudi ne da kashi 1.7% a kasuwannin Duniya. Wannan ya faru ne bayan kasar Saudi ta nada Yarima a matsayin sabon Ministan fetur a kasar.

Abdulaziz Salman wanda ya dade a matsayin Wakilin Saudi a gaban OPEC shi ne ke kan kujerar Minista yanzu inda ya alwashi ba za su rage yawan man fetur da kasashe su ke hakowa ba.

Yarima Salman ya hakikance a kan cewa Saudi za ta cigaba da hako miliyan 1.2 na gangar danyan mai kullum. A da an yi tunani rage adadin man da ake hakowa zai kara darajarsa.

‘Dan gidan Sarkin ya kuma ce nan gaba za a ga tasirin yarjejeniyar da aka shirya tsakanin kungiyar OPEC ta kasashen da ke hako danyan man fetur da kuma sauran baren kasashe.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya ba su so a taba masu babban tulun samun kudinsu

Abin da wannan karin kudi na fiye da 1% ya ke nufi shi ne kudi za su kara shigowa Najeriya bayan fetur ya kara tsada. Man fetur ya na cikin hanyoyin da gwamnatin Najeriya ta ke samun shiga.

Yanzu haka gwamnati ta na kokarin ganin ta shirya kasafin kudin shekara mai zuwa. Gwamnatin tarayya ta na sa ran saida gangar mai ne a kan $55 inda duk rana za a hako miliyoyin ganguna.

Idan aka shiga wannan makon da karin farashi, babu shakka wannan ne babban tashin gauron zabin da mai ya yi tun a Watan Yulin shekarar nan. Wannan zai yi wa Najeriya da wasu dadi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel