Nadin mukamai: Ganduje ya fadi dalilin da ya sa har yanzu bai nada kwamishinoni ba

Nadin mukamai: Ganduje ya fadi dalilin da ya sa har yanzu bai nada kwamishinoni ba

Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fadi dalilin da ya kawo masa tsaiko wurin nadin kwamishinoni bayan kimanin watanni hudu da rantsar da shi a karo na biyu.

Gwamnan ya ce ya na daukan lokacinsa ne domin zakulo ‘yan wasu jam’iyyun da suka ba shi gudunmuwa har ya samu nasarar sake koma mulki a karo na biyu.

KU KARANTA:Kuyi watsi da faifan audio dake cewa ana rikici a hanyar Kaduna-Abuja, inji Gwamnatin Kaduna

Jaridar The Nation ta tattaro mana bayanai cewa rashin nadin kwamishinonin bai rasa nasaba ga sakayya da gwamnan yake son yiwa dukkanin jam’iyyun da suka mara masa baya lokacin zabe.

A wa’adinsa na farko, Gwamna Ganduje ya nada kwamishinoninsa ne bayan an rantsar da shi da makonni uku kacal.

Har wa yau, Ganduje ya bayyana son ganin ya bai wa ko wace jam’iyya hakkinta daga cikin wadanda suka mara masa baya a matsayin abinda ya sanya har yanzu bai nada kwamishinonin ba.

Ganduje ya fadi wannan maganar ne a cikin wata hira da yayi a wani gidan rediyon Kano, inda ya ce nan bada jimawa ba zai fitar da sunayen kwamishinoninsa.

“Wasu daga cikin tsoffin kwamishinonina za su sake komawa yayin da wasunsu ba za su koma ba. Wadanda ma ba su samu komawa ba zamu samar masu wuraren da zasu rike domin su kasance tare da gwamnatinmu.” Inji Gwamnan.

Al’amarin nadin kwamishinonin ya sha bamban da na shekarar 2015 a dalilin hadin gwiwa da gwamnan ya samu lokacin zaben 2019.

https://thenationonlineng.net/why-im-yet-to-form-my-cabinet-by-ganduje/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel