Kuyi watsi da faifan audio dake cewa ana rikici a hanyar Kaduna-Abuja, inji Gwamnatin Kaduna

Kuyi watsi da faifan audio dake cewa ana rikici a hanyar Kaduna-Abuja, inji Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata wani faifan audio dake yawo yana gargadin mutane da cewa su guji bin hanyar Kaduna-Abuja saboda ana rikici.

Faifan audio dai ya kai tsawon sakan 46 inda a cikinsa a ke fadin hankali ba a kwance yake a wannan hanyar ta Kaduna-Abuja.

KU KARANTA:Zamu kai karar masu rubuta labaran karya a kan jiharmu kotu – El-Rufai

Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaro da kuma harkokin cikin gida na jihar Kaduna ne ya karyata wannan magana a cikin wani zancen da fitar ranar Asabar 14 ga watan Satumba, inda ya ce jami’an tsaro na nan na bin sahun inda wannan wannan faifan audio ya fito.

Ya kara da cewa, hukumar kula da tsaron jihar Kaduna na kira ga ilahirin al’ummar jihar musamman masu zirga-zirga bisa hanyar da suyi watsi da faifan su cigaba da harkokinsu saboda maganar dake ciki karyar banza ce kawai.

Har ila yau, ya nemi al’ummar idan akwai wani da ya san wanda ya kirkiri wannan labari da yayi gaggawar sanar da jami’an tsaro domin a dauki mataki a kansa.

A wani labarin makamancin wannan zaku ji cewa, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi gargadi ga masu watsa labaran karya game da jiharsa.

A cikin zancensa ya ce duka wanda ya yada labaran karya game da Kaduna, zai tsinci kansa a gaban kotu kuwa. Gwamnan yayi wannan gargadin ne a Abuja ranar Talata wurin bikin wallafa wani littafi da Japheth Omojuwa ya rubuta.

https://www.dailytrust.com.ng/disregard-audio-of-killings-along-kaduna-abuja-road.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel