Gwamnatin Buhari za ta samar da tabbatacciyar wutar lantarki – Minista

Gwamnatin Buhari za ta samar da tabbatacciyar wutar lantarki – Minista

Engr. Saleh Mamman, ministan lantarki ya ce kudurin Shugaba Muhammadu Buhari na ‘Next Level’ zai samar da tabbatacciyar wutar lantarki a Najeriya kafin karshen wa’adinsa na biyu.

Shugaban kamfanin bayar da wutar lantarkin na KAEDCO, Engr. Garba Haruna ya ce kamfaninsu a shirye yake domin marawa gwamnati baya wurin cinma burinta na daidaita wutar Najeriya.

KU KARANTA:Buhari ya bada zunzurutun kudi domin yin aikin tituna 14 a Najeriya

Ministan lantarkin tare da karamin ministan ma’aikatar wutar lantarki Mista Jeddy Agba sun je birnin Kadunan ne domin wata ziyarar aiki ta kwana biyu.

Ministan bayan ya ziyarci tashar wutan Mando mai karfin 330KV da kuma tashar Kudenda, ya ce ma’aikatarsa za tayi iya bakin kokarinta domin ganin an kammala dukkanin ayyukan da ake a karkashin ma’aikatar domin bai wa Najeriya lantarki.

Ya kuma yi kira ga kamfanin dake da alhakin raba lantarkin da suyi amfani da tashar Kudenda wadda saura kiris a kammala aikinta domin bayar da lantarki yadda ya kamata.

Da yake martani game da batun ministan, Daraktan KAEDCO, Engr. Garba Haruna ya ce kamfaninsu a shirye yake da marawa gwamnati baya wurin bai wa jama’a lantarki da aka samu daga tashoshinta.

Daraktan wanda ya samu wakilcin wani jami’in ma’aikatar, Raul Kumar ya yabawa gwamnatin tarayya a bisa kokarinta na ganin ta kammala ayyukan da suke shafi ma’aikatar lantarkin Najeriya.

A cewarsa, idan har aka kammala aikin ko shakka babu wutar lantarki za ta wadata a Najeriya fiye da yadda ake samunta a yanzu.

https://thenationonlineng.net/buharis-govt-will-deliver-uninterrupted-power-minister/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel