Zaben gwamna: Gwamna Abiodun ya lallasa Akinlade yayinda kotun zabe ta soke karar da ke kalubalantar takardunsa

Zaben gwamna: Gwamna Abiodun ya lallasa Akinlade yayinda kotun zabe ta soke karar da ke kalubalantar takardunsa

Dan takarar jam’iyyar Allied People’s Movement (APM), Adekunle Akinlade, a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, ya sha babban kaye yayinda kotun zaben gwamna na jihar Ogun karkashin jagorancin Yusuf Halilu, ta soke karar da ya shigar inda yake kalubalantar takardun makarantar Gwamna Abiodun.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Akinlade ya nemi a tsige Gwamna Dapo Abiodun kan hujjar gabatar da takardun makaranta na karya.

Da take zartar da hukunci, kotun zaben ta bayyana cewa kotun daukaka karat a riga ta kawo karshen batun takardar karatun Abiodun, don haka, tace ba za a iya bari mai kara ya sake bude babin wannan lamarin ba a kotun zabe, tunda kotun daukaka kara ta kasha wannan wutar.

Kotun zaben ta bayyana cewa za ta tsaya akan hukuncin kotun daukaka karar, inda ta kara da cewa mai karan ya kuma cike takarda inda yake kalubalantar takardun Abiodun a bayan lokacin da aka yarda dashi.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani mutum ya fille kan dan achaba, ya kuma cire kayan cikinsa a jihar Neja

A wani labarin kuma mun ji cewa Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu ya ce an damfari jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar kan cewa hukumar zabe INEC ta adana sakamakon zabe a cikin rumbun ajiyar sakamakon zabe wato server.

Daily Trust ta ruwaito cewa Salihu ya yi wannan jawabin ne yayin hira da ya yi da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar Adamawa inda ya ce hukucin da kotun ta yanke ya nuna cewa babu wani doka da ya bawa INEC ikon ajiye sakamakon zabe a server.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel