Buhari ya bada zunzurutun kudi domin yin aikin tituna 14 a Najeriya

Buhari ya bada zunzurutun kudi domin yin aikin tituna 14 a Najeriya

Majalisar FEC ta aminta da fitar da naira biliyan 166 domin yin tituna 14 a wurare daban-daban cikin Najeriya.

A cigaba da kokarin gwamnati na kawo cigaba a fannin tattalin arziki da kuma sufuri, majalisar zartarwa ta fitar da biliyan N166 domin kwaskwarima da kuma yin sabbin tituna 14 a Najeriya.

KU KARANTA:Zaben gwamnan Kogi: Mutum 10 daga cikin ‘yan G-12 sun goyi bayan Wada

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya karanto takardar da ke dauke da bukatar yin wannan aikin. Ma’akatar ayyuka da gidaje ce ta shirya daftarin dauke tun ranar 3 ga watan Satumba.

Manufar samar da hanyoyin masu kyau ya ta’allaka ne domin samawa matafiya musamman masu kasuwanci sauki daukan kaya daga wuri zuwa wuri.

Daga cikin titunan da aka lissafa wannan aikin zai shafa akwai, titin Kontagora-Rijau dake jihar Neja inda za a gina har da gada guda biyu. Titin Kano-Katsina, inda za a kara fadin titin daga shataletalen Dawanau.

Titin Kontagora-Bangi, titin Bonny Camp da kuma gadar Eko har zuwa gadar Apongbon ta jihar Legas. Titin Irrua-Edenu-Udomi-Uwessan wanda za a yiwa kwaskwarima jihar Edo, Ilobu-Erinle tsakanin Kwara da Osun.

Haka zalika akwai gadar Wudil wadda take sadarwa zuwa Gaban Komi kan bypass din hanyar Maiduguri a jihar Kano. Baya ga wadannan hanyoyin akwai tituna da yawa wadanda gwamnatin tarayya za tayi aiki a kansu a jihohin Jigawa, Yobe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.

https://web.facebook.com/100004659850594/posts/1394547427377239/?_rdc=1&_rdr

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel