'Yan sandan jihar Neja sun kama 'yan bangar siyasa 62

'Yan sandan jihar Neja sun kama 'yan bangar siyasa 62

- Hukumar 'yan sandan jihar Niger ta kama 'yan bangar siyasa 63 yayin zaben fidda gwanin shuwagabannin kananan hukumomi da aka yi a jihar

- Hukumar ta kama mota kirar Toyota dankare da miyagun makamai a hannun wadanda ake zargin

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya ja kunnen 'yan siyasa akan daukar nauyin hargitsi da hayaniya yayin neman kujerun mulki

Hukumar 'yan sandan jihar Niger sun cafke 'yan bangar siyasa 62 da suka kai hari yayin zaben fidda gwanin shuwagabannin kananan hukumomi.

Jam'iyyar APC ta kammala zaben fidda gwani na shuwagabannin kananan hukumomi da gudumomin jihar don shirin zaben 30 ga watan Nuwamba a jihar.

Alhaji Adamu Usman, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya sanar da kamfanin dillancin labarai a ranar Lahadi cikin garin Minna.

Kwamishinan 'yan sandan yace wadanda ake zargin daga kananan hukumomi 5 na jihar suke.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ya kashe matarsa har lahira akan kin shayarda jinjirinsu

"Mutane 44 daga karamar hukumar Paikoro; 4 daga karamar hukumar Rijau; mutane 10 daga karamar hukumar Tafa; mutane 2 daga karamar hukumar Katcha sai kuma mutane 2 daga karamar hukumar Rafi," inji kwamishinan 'yan sandan.

Ya yi bayanin yadda suka kama mota kirar Toyota a makare da miyagun makamai a wajen wadanda ake zargin.

Kwamishinan yace za a tura wadanda ake zargin zuwa kotu akan laifin tada zaune tsaye, kamasu da miyagun makamai da goyon bayan ta'addanci.

Usman ya ja kunnen 'yan siyasa masu neman kujerun mulki da su guji daukar nauyin hargitsi yayin da bayan zaben kananan hukumomin da za a yi a jihar.

Yace hukumar shirye take don samar da zaman lafiya mai dorewa yayin gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel