Gwamnatin Kaduna za ta kori mutanen da ba malaman makaranta bane amma suke zaune a gidajen malamai

Gwamnatin Kaduna za ta kori mutanen da ba malaman makaranta bane amma suke zaune a gidajen malamai

- Gwamnatin jihar Kaduna, tayi kira ga mutanen gari mazauna gidajen malaman makaranta

- Ta bukaci su gaggauta barin gidajen da aka gina don malaman makaranta kadai

- Gwamnatin tace tana iyakar kokarinta wajen ganin ta gyara makarantun gwamnatin da ke fadin jihar

Gwamnatin jihar Kaduna na kira ga mutanen da ke zama a gidajen malaman gwamnatin jihar da su tattara su bar gidajen.

Gwamnatin jihar, ta kwamishinan ilimi, Dr Shehu Mohammed Makarfi yace gidajen an ginasu ne a cikin makarantun don malamai ba wai don mutanen gari ba. A don haka ne gwamnatin jihar ba zata lamunci hakan ba.

Ya lissafo makarantu kamar su kwalejin sarauniya Amina, kwalejin Rimi da kwalejin gwamnatin jihar Kaduna inda mutanen gari ke zama wadanda ba malamai ba.

"Ba zamu lamunci mutanen da ba malaman makaranta ba na zama a gidajen makaranta. A don haka ne muka tura musu da bukatar su tashi daga gidajen da aka gina don ma'aikatan makaranta." Inji shi.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

Kwamishinan ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan rediyon jihar Kaduna wanda ake yi duk ranar Asabar.

Ya kara da cewa, ma'aikatarsa bazata zura idanu ha irin wadannan mutanen ba saboda akwai bukatar malamai su zauna kusa da dalibansu.

Dr Shehu Makarfi yace gwamnatin jihar na yin iyakar kokarinta don ganin ta gyara makarantun gwamnatin da ke fadin jihar amma akwai bukatar iyaye da mazauna makarantun da su bada goyon baya ta hanyar kare kayayyakin aiki a makarantun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel