Da duminsa: Tsohuwar ministar Buhari ta sauya sheka zuwa PDP

Da duminsa: Tsohuwar ministar Buhari ta sauya sheka zuwa PDP

Tsohuwar ministar lamuran matan Najeriya, Aisha Jummai Alhassan ta sauya sheka da jam’iyyar UDP zuwa PDP.

Tsohuwar ministar wadda ta tsaya takarar gwamnan Taraba a zaben 2019 karkashin jam’iyyar ta UDP, ta dauki wannan matakin na sauya sheka ne bayan wata ganawa da shugabannin jam’iyyar UDP a Jalingo.

KU KARANTA:An fara gudanar da bincike a asirce game da asusun bankin Lawan da Gbajabiamila

Bayan kammala ganawar ne aka karanto wata yarjeniya da ‘ya’yan jam’iyyar wadanda suka fito daga shiyyoyi 168 cikin kananan hukumomi 16 suka aminta da barin jam’iyyar domin komawa PDP.

Ta ce bisa ga rinjaye mafi yawa daga jam’iyyar babu abinda za ta face ta bi ayari zuwa jam’iyyar ta PDP. An gudanar da wannan ganawar ne a gidan tsohuwar ministar dake Jalingo.

Kuma taron ya samu halartar mambobin jam’iyyar UDP daga kananan hukumomi 16 dake jihar Taraba. Idan baku manta ba dai an dakatar da Aisha Jummai Alhassan ne daga jam’iyyar APC ana daf da zaben 2019, inda ake zarginta da yiwa jam’iyya zamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel