Zaben gwamnan Kogi: Mutum 10 daga cikin ‘yan G-12 sun goyi bayan Wada

Zaben gwamnan Kogi: Mutum 10 daga cikin ‘yan G-12 sun goyi bayan Wada

A daidai lokacin da shirye-shirye ke dada kankama domin tunkarar zaben Gwamnan Kogi da za ayi a ranar 16 ga watan Nuwamba, tsoffin ‘yan takarar kujerar gwamnan a PDP su 10 sun yi mubaya’a ga Engr. Musa Wada.

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada shi ne jagoran wannan tawaga wadda tayi mubaya’a ga Musa Wada a ranar Juma’a 13 ga watan Satumba, 2019.

KU KARANTA:Da duminsa: Tsohuwar ministar Buhari ta sauya sheka zuwa PDP

Tsohon dan takarar gwamnan PDP a jihar, Alhaji Muhammad Shuaibu ne ya fitar da wannan sanarwa cikin wata hira da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a madadin sauran tsoffin ‘yan takarar, Shuaibu ya bayyana dalilin da ya sa suka ga ya zama wajibi a garesu su yiwa jam’iyyarsu aiki domin cin nasara.

“A matsayina na daya daga cikin ‘yan kungiyar G12 Kogi PDP, mun lura cewa hadin kanmu a daidai wannan lokaci shi ne ya fi komi muhimmanci.

“Wannan dalilin ne ya sanya mu yiwa Engr. Musa Wada mubaya’a saboda babban burinmu shi ne ciyar da jiharmu Kogi gaba.

“Bayan ganin irin shiri da kuma tanadin da Musa Wada yake da shi game da wannan mulki ya sanya kungiyar G12 Kogi PDP ta mara masa baya ba tare da wata shakka ba. Manufar kuma a nan duk ba ta wuce cigaban PDP da kuma jiharmu ta Kogi ba.” Inji Shuaibu.

Haka zalika, yayi kira ga sauran ‘yan kungiyar ta G12 Kogi da su kasance jakadu ga dan-takarar domin samun nasara a zaben gwamnan jihar dake tafe cikin watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel