Dan hakin da ka raina: Yayi kokarin yaci zalinta, ashe 'yar dambe ce bai sani ba, ita kuwa tayi ta jibgarsa kamar Allah ne ya turo ta

Dan hakin da ka raina: Yayi kokarin yaci zalinta, ashe 'yar dambe ce bai sani ba, ita kuwa tayi ta jibgarsa kamar Allah ne ya turo ta

- Idan zaka yiwa mutum kwace ka fara tabbatarwa bai fi karfin ka ba, ko kuma ka tabbatar da cewa ba dan dambe bane

- Wannan darasi a wajen wani dan daba a garin Rio De Janeiro a lokacin da yayi kuskuren yiwa wata budurwa kwace a wajen gidanta

- Ashe dai yayi kuskuren da bai taba yi bane a rayuwarshi, domin kuwa 'yar dambe ya tare mai suna Polyana Viana

Viana ta bayyana abinda ya faru da ita a daren ranar Asabar din da ta gabata, inda ta ce: "Da yaga cewa na ganshi sai ya zauna kusa dani, ta cigaba da cewa "Ya tambayeni lokaci na fada masa, duk da haka yaki tashi ya tafi.

"Sai nayi kokarin sanya wayata a aljihu, sai yace bani wayarki, karma kiyi kokarin yin wani abu domin ina da makami a jikina, sai ya sanya hannunshi akan bindiga, sai na gane cewa ta bogi ce.

KU KARANTA: Ko jibgi na jibga, ku karya na karyawa, amma banda kisa - Hukuncin da shugaban kasar Philippine ya cewa mutanen shi su dauka kan barayin ma'aikata

"Yana kusa dani sosai, sai na gane cewa idan har bindiga ce bashi da damar da zai iya ciro ta, sai na tashi cikin gaggawa na kai masa naushi da mangari, sai ya fadi kasa, sai na shake masa wuya, sai na kama shi na zaunar dashi a wajen da muke zaune na fada mishi, yanzu sai mu jira 'yan sanda ko."

Viana ta ce ta taba dukan wasu maza guda biyu akan babur da suka so su kwace mata wata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel