Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa birnin Ouagadougou, an masa tarbar karamci

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa birnin Ouagadougou, an masa tarbar karamci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Burkina Faso domin hallarton taron Kungiyar Bunkasa Tattalin Arziki na Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da za a gudanar a babban birnin kasar, Ouagadougou.

Kamar yadda hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad ya sanar a shafinsa na Twitter, ana sa ran shugaban kasar zai dawo babban Abuja da zarar an kammala taron.

Da isarsa, Shugaba Roch Marc Christian Kaboré da tawagarsa suka tarbe shi a filin saukan jirage cikin wani yanayi mai ban sha'awa.

Kazalika, wasu 'yan Najeriya mazauna kasar na Burkina Faso sun fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Shugaba Buhari. Sun fito rike da tutar Najeriya suna rera wakoki na yabo da farin ciki.

Shugaba Buhari ya tafi taron tare da wasu gwamnonin Najeriya.

Ga bidiyon yadda aka tarbi shugaban kasa a kasa kamar yadda hadiman shugaban kasa, Lauretta Onochie ta wallafa a shafinta na Twitter.

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel