'Yan damfara ne suka yaudari Atiku da PDP kan batun 'server' - Jam'iyyar APC

'Yan damfara ne suka yaudari Atiku da PDP kan batun 'server' - Jam'iyyar APC

- Jigo a jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Mustapha Salihu ya ce 'yan damfara ne suka yaudari jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar kan batun 'server'

- Kwamared Salihu ya ce kotu ta tabbatar cewa babu wani doka ta ya bawa INEC damar ajiye sakamakon zabe a wani rumbun ajiya wato 'server'

- Kwamared Salihu ya ce babu yadda zai yiwu a ce mutumin da zama Janar a soja, kuma ya yi minista ya kuma zama shugaban kasa ba shi da takardun makaranta

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu ya ce an damfari jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar kan cewa hukumar zabe INEC ta adana sakamakon zabe a cikin rumbun ajiyar sakamakon zabe wato server.

Daily Trust ta ruwaito cewa Salihu ya yi wannan jawabin ne yayin hira da ya yi da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar Adamawa inda ya ce hukucin da kotun ta yanke ya nuna cewa babu wani doka da ya bawa INEC ikon ajiye sakamakon zabe a server.

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Ya ce, "wasu mutane ne kawai suka damfare su, sun amshe musu kudade sun fada musu cewa akwai wata rumbum ajiyar sakamakon zabe na INEC alhalin hakan ba gaskiya bane, hakan yasa suka gaza gabatar da hujojin kare wannan ikirarin.

"Duk da cewa lauyoyinsu sunyi kokari wurin yayin shari'ar, anyi watsi da karar saboda babu wasu kwararran hujojji. Wannan nasara ce da dukkan 'yan Najeriya ba wai APC kadai ba. Yanzun mun kawar da duk wani abu da ke dauke mana hankali kuma gwamnati za ta fara kwararawa al'umma romon demokradiyya.

"Dama munyi tsamanin wannan sakamakon daga kotu. Dukkan kararrakin da jam'iyyar hamayyar suka shigar ba su da inganci saboda babu yadda za ka ce Janar din Soja wanda ya yi shugaban kasa, ya yi minista kuma ya sake yin shugabancin kasa na shekaru hudu ba shi da takardun makaranta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel