An fara gudanar da bincike a asirce game da asusun bankin Lawan da Gbajabiamila

An fara gudanar da bincike a asirce game da asusun bankin Lawan da Gbajabiamila

Hukumar kula da kudade ta NFIU ta soma gudanar da bincike a kan asusun bankin shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad da mataimakinsa Ovie Omo-Agege.

NFIU ta fara gudanar da wani bincike game da asusun bankin da shugabannin majalisar dokokin ke ajiyar kudi.

KU KARANTA:Zamu kai karar masu rubuta labaran karya a kan jiharmu kotu – El-Rufai

Wadanda wannan binciken ya shafa sun hada da; Shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase da sauran masu rike da mukamai a cikin majalisun biyu.

Hukumar tana kan gudanar da irin wannan binciken game da asusun bankin Alkalin-alkalan Najeriya, Jastis Muhammad Tanko.

Haka zalika, asusun bankin wasu manya-manyan ‘yan siyasa suna fuskantar irin wannan binciken. NFIU ta cinma wani mataki na musamman a fannin binciken da take yi inda ta aika sunayen mutanen da take binciken a kansu zuwa ga dukkanin bankunan Najeriya.

Wasikar da wani daraktan bincike na NFIU, Fehintola Salisu, ya rubuta ta sanya ranar Juma’a 13 ga watan Satumba a matsayin ranar karshe da take son bankunan su bada hadin kai game da bukatar ta su.

A cikin wasikar ya hukumar ta ambaci sunayen Majalisar dokokin tarayya, ma’aikatar shari’ar Najeriya, dukkanin asusun bankin masu rike da mukamai a majalisar dokokin Najeriya.

A bangare guda kuwa, Babban daraktan NFIU Modibbo Tukur, ya ce shi baida masaniya game da wannan wasikar, kana kuma ya ce za a hukunta bankunan da suka fara fitar da wannan labari.

“Idan kuka lura zaku bani bane na sanyawa wasikar hannu, a don haka bincike ne na sirri wanda yada kan iya zama laifi. Daraktan da kaga ya rubuta wasikar kuma ya sanya mata hannu shi ke kula da binciken hukumar NFIU.” A cewar Modibbo.

https://www.pmnewsnigeria.com/2019/09/14/bank-accounts-of-lawan-gbajabiamila-others-under-investigation/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel