Mata sun lakada wa mijinsu duka saboda zai kara mata ta uku

Mata sun lakada wa mijinsu duka saboda zai kara mata ta uku

- Wani mutum dan kasar Indiya, Danesh ya sha duka a wurin matansu biyu saboda ya yi yunkurin kara mata ta uku ba bisa ka'ida ba

- Kafin afkuwar wannan lamarin, mata biyu ba su san cewa su kishiyoyi bane

- Wasu mutanen gari sun taya matansa dukansa kafin daga bisani a mika shi hannun 'yan sanda

Wani mutum mai shekaru 26 dan kasar Indiya mai suna Dinesh ya jefa kansa cikin rikici yayin da ya yi yunkurin kara mata ta uku amma ba bisa ka'ida ba.

Legit.ng ta ruwaiti cewa matansa na aure biyu sun hada kai sun lakada masa duka yayin da suka gano zai kara aure. Dinesh ya yi auren farko ne a 2016 kafin daga bisani ya auri wata matar ta uku a 2019.

Daily Mail ta ruwaito cewa Dinesh ya na dukkan matansa biyu hakan yasa suka koma gidan iyayensu.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari a kotu: Wani dan PDP ya cakawa dan APC kwalba

Sai dai matan biyu da ya aura da farko ba su san cewa su kishiyoyi bane domin tsamaninsu Dinesh mata daya kawai ya aura.

Amma da suka gano cewa mijinsu mata biyu ya aura kuma yana shirin kara auren ta uku, sai suka dauki tsatsauran mataki a kan sa.

Faifan bidiyon ya nuna matan biyu suna bin Danesh shi kuma yana kokarin tserewa.

Wasu mutane su ma sun taya matan dukkansa kafin daga bisani aka mika shi hannun jami'an 'yan sada.

A addinin Hindu haramun ne miji ya auri mata fiye da guda daya tun shekarar 1956 amma musulmi suna iya auren har mata hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel