Gwamnatin jihar Kaduna ta kori daraktoci biyu KSDPC

Gwamnatin jihar Kaduna ta kori daraktoci biyu KSDPC

- Gwamnatin jihar Kaduna ta kori daraktoci biyu na kamfanin habaka kadarori KSDPC na jihar

- Babban mai baiwa gwamnatin jihar shawara a fannin yada labarai ya sanar da hakan

- Gwamnatin ta soke duk filayen da aka bada daga hukumar tun daga 29 ga watan Mayu, 2015

A jiya ne gwamnatin jihar Kaduna ta kori daraktoci biyu na kamfanin habaka kadarori (KSDPC) na jihar Kaduna.

Daraktocin su ne: Daniel Z. Kambai (bangaren aiyuka) da Yusuf Bala Mohammed ( bangaren kudi).

Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamnan shawara ta musamman akan harkokin yada labarai, ya sanar da sallamar a maganar da yayi ga manema labarai.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

A zancen da ya fito daga gidan Sir Kashim Ibrahim, yace gwamnatin ta fara shirin gyaran KSDPC ta hanyar zaben sabon babban manaja.

Gwamnatin ta kara da sanarwar cewa ta kwace duk filayen da aka bada tun daga 29 ga watan Mayu, 2015.

Gwamnatin tace an bada filayen ne ba tare da bin dokar bayar dasu ba, a don haka ne ta kwacesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel