Zamu kai karar masu rubuta labaran karya a kan jiharmu kotu – El-Rufai

Zamu kai karar masu rubuta labaran karya a kan jiharmu kotu – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce rashin zaman mutum a Kaduna ba zai hana a tasa keyarsa zuwa gaban kotu ba idan har ya na yada labaran karya game da jihar.

El-Rufai ya fadi wannan maganar ne ranar Talata a Abuja wurin bikin wallafa wani littafi mai suna ‘Digital Wealth’ wanda Japheth Omojuwa ya rubuta.

KU KARANTA:Abinda Buhari ya tattauna da Gwamnonin APC ranar Juma’a a Abuja

A cewar gwamnan, da asalin masu wallafa labaran a tuwita da kuma wadanda ke sake yadawa abinda ake cewa re-tweet za su jefa kansu cikin matsala idan har labarin yayi sanadiyar rasa rayuka ko kuma sanya mutane cikin rudani.

Haka zalika, ya kara da cewa ana iya amfani da shafukan sada zumunta domin yin abu mai amfani haka kuma idan ba ayi amfani da shi ta hanyar da ya dace ba zai kawo aibu.

El-Rufai ya ce: “Kada mu hada ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin kisan rayuka, idan ka rubuta labarin karya zai iya sanadiyar kashe-kashe da baka san adadinsu ba. A dalilin wannan akwai bukatar ka gurfana gaban kotu domin amsa jawabi a kan kashe-kashen da ka haddasa.

“A jihar Kaduna, mun dauki matakai tsaurara game da wannan abu. Saboda a sakamakon yada labaran karya a shafukan sadarwa na zamani mutane da dama sun rasa rayukansu.

“Hakan ne ya sa muka tashe tsaye akan wannan mummunan aiki, babu yadda za ayi kana Legas ko Fatakwal ka rika bada labarin abinda ke aukuwa a Kaduna. Zamu kai mutum gaban alkali domin a zartar masa da hukunci.” A cewar El-Rufai.

https://punchng.com/well-force-lagos-based-fake-news-peddlers-to-kaduna-trial-el-rufai/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel