Toh fah: NFIU ta nemi bayanai kan asusun ajiyar bankin wasu alkalai da 'yan majalisa

Toh fah: NFIU ta nemi bayanai kan asusun ajiyar bankin wasu alkalai da 'yan majalisa

- Sashen binciken kudi ya bukaci bayanan asusun bankunan manyan jami'an kasar nan

- A wasikar da sashen ya mika ga bankunan, bai sanar da dalilin yin hakan ba

- Manyan kasar sun hada da 'yan majalisar tarayya har da jami'an ma'aikatar shari'a ta kasa

Sashen binciken kudi, NFIU, ta bukaci bankuna da su tura bayanan asusun bankunan 'yan majalisu da ma'aikatan shari'a na kasar nan.

The Cable ta ruwaito cewa ta ga wasikar mai kwanan wata 10 ga Satumba, 2019 wacce sashen binciken kudin ke bukatar lambobi da sunayen asusun bankunan jami'an.

Sashen binciken kudin bai bada dalilin bukatarsa ba a wasikar da Fehintola Salisu, daraktan kiyasi na hukumar yasa hannu.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

Wasikar an mika ta ne ga shuwagabannin bankuna.

An rubuta wasikar kamar haka: Bukatar bayanan asusun bankunan: 'Yan majalisar tarayya, jami'an ma'aikatar shari'a ta kasa, NJC, manyan jami'an kamashon majalisar dattawa da kuma manyan alkalai."

"Sashen binciken kudi na NFIU na bukatar sunaye da lambobin asusun bankunan 'yan majalisar dattawa, jami'an ma'aikatar shari'a da sauran manyan 'yan siyasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel