Tirkashi: Ya kashe matarsa har lahira akan kin shayarda jinjirinsu

Tirkashi: Ya kashe matarsa har lahira akan kin shayarda jinjirinsu

- Wani mutum mai suna Kingsley Madukwe ya kashe matarsa har lahira a kan kin shayarda jinjirinsu

- Kingsley yace mari ya zabga mata wanda sakamakon hakan yasa ta fadi kasa sai mutuwa

- Tuni dai hukumar 'yan sanda suka cafkesa kuma ana cigaba da gudanar da bincike

Hukumar 'yan sandan jihar Ogun, ta damke Kingsley Madukwe mai shekaru 40 akan zarginsa da ake da kashe matarsa har lahira.

Kingsley ya zabgawa matarsa Glory mai 'ya'ya 8 mari bayan taki shayar da jinjirinsu.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abimbola Oyeyemi, ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Wanda ake zargin mai sana'ar achaba, ya fusata ne bayan da marigayiyar matarsa taki shayarda jinjirinsu.

Ya jawota tare da zabga mata mari bayan da tayi yunkurin barin dakin barcinsu. Bayan marin ne matar tasa ta fadi inda a take ta mutu.

KU KARANTA: 'Yan duba sun damfari wata mata naira miliyan 11

Oyeyemi yace an cafke wanda ake zargin a ranar Laraba bayan rahoton da Chief Rafiu Gbadamosi ya kaiwa 'yan sandan.

Oyeyemi yace, "Sakamakon rahoton ne SP Salau Abiodun, ya jagoranci masu bincike zuwa inda mummunan abun ya faru, wanda a take suka cafke wanda ake zargin."

"Bayan bincike, mun gano cewa wanda ake zargin mai sana'ar achaba, Dan asalin Ihiala ne a jihar Anambra. Yace matarsa wacce suke da yara 8 tana da jinjiri mai watanni 8. Kukan jinjirin ya tadasa barci inda ya tashi matar don shayarda jinjirin. Amma sai tace ta gaji bazata iya shayar da jinjirin ba."

"Yace ta mike don barin dakin barcinsu sai ya jawota tare da zabga mata mari. A take ta fadi tare da cewa ga garinku. A yanzu haka gawar matar tana wajen ajiye gawarwaki a asibitin Ota don bincike."

Jami'in hulda da jama'ar hukumar 'yan sandan yace, kwamishinan 'yan sandan jihar, Bashir Makama, ya umarci da a mika mutumin zuwa bangaren binciken laifukan kisa don bincike da gurfanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel