Abinda Buhari ya tattauna da Gwamnonin APC ranar Juma’a a Abuja

Abinda Buhari ya tattauna da Gwamnonin APC ranar Juma’a a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga jagororin jam’iyyar APC da su yiwa jam’iyyar tsarin da za ta cigaba da mulkin Najeriya bayan saukarsu.

“Akwai bukatar mu kafa jam’iyyar APC tayi karfin da za ta iya cigaba da mulki ko baya bamu nan.” Inji Shugaban kasa.

Buhari yayi wannan furucin a fadar Villa ranar Juma’a lokacin da yake tattaunawa da shuwagabannin APC da kuma dukkanin gwamnonin APC na jihohin Najeriya.

KU KARANTA:Wata tankar man fetur ta kife a kan hanyar dake tsakanin Enugu-Abakaliki

Ya fadawa bakin nasa cewa, taron FEC na ranar Laraba shi ne ya dauke hankalinsa daga kan shari’arsa da Atiku dake gudana a kotu.

A nashi jawabin a wurin taron, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya jinjinawa kotun zaben a kan hukuncin da ta yanke, inda ya ce, “gaskiya ce kawai tayi halinta ba komi ba”.

“Ko kadan bamu taba yin kokwanto ba. Mun gamsu da wannan nasara da muka samu.” Inji Adams. A nashi jawabin kuwa, shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya taya Shuagban kasan murna a madadin sauran gwamnonin.

A lokacin da yake karin bayani game da nasarar kotun, Bagudu ya ce: “Gaba dayanmu gwamnonin APC mun zo nan ne domin tayaka murnar nasara wadda ka samu a kotun zabe ranar Laraba.

“Hukuncin ya matukar faranta mana rai, a don haka a madadin dukkanin gwamnonin APC ina tayaka murna da samun wannan nasara.” Inji Bagudu.

https://punchng.com/lets-institutionalise-apc-so-that-when-we-leave-itll-continue-to-lead-buhari/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel