Mutuwar Mugabe: Osinbajo zai wakilci Buhari a wajen bikin birneshi a kasar Zimbabwe

Mutuwar Mugabe: Osinbajo zai wakilci Buhari a wajen bikin birneshi a kasar Zimbabwe

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai samu daman halartar bikin birne tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ba, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

A ranar Asabar, 14 ga watan Satumba ne za’a binne Robert Mugabe, kuma shugaban kasa Buhari ya wakilta mataimakin Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai wakilceshi a yayin wannan babban taro.

KU KARANTA; Dahiru Bauchi ya yi karin haske game da harbe harben da aka yi a gidansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba ta shafinta na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda tace:

“Mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo zai wakilcishugaban kasa Muhammadu Buhari a jana’izar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, a gobe Asabar, Osinbajo zai jera kafada da kafada da sauran shuwagabannin kasashen Afirka a wajen jana’izar da za’a yi a babban filin wasa na kasar dake Harare.

“Daga cikin shuwagabannin da za su halarci jana’izar akwai shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta of Kenya. Osinbajo zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatin Najeriya, kuma ana sa ran zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar.” Inji sanarwar.

Marigayi tsohon shugaban kasa Mugabe na daga cikin shuwagabannin da suka halarci bikin nadin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, kuma sun cigaba da kyakkyawar alaka har lokacin da aka kifar da gwamnatinsa a shekarar 2017.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel