Bangaren da Kashamu ke jagoranta sun bar PDP, sun koma APC

Bangaren da Kashamu ke jagoranta sun bar PDP, sun koma APC

Akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sama da 1000 daga yankin mazabar Ogun ta gabas, masu biyayya ga bangaren Buruji Kashamu ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba.

Mista Tunji Egbetokun Babban mai ba gwamna Dapo Abiodun shawara akan harkokin siyasa ne ya tarbi wadanda suka sauya shekar a Abeokuta, inda suka bayyana cewa sun dauki shawaran ne don nuna goyon baya ga Gwamnan.

Egbetokun, wanda ya tsaya a matsayin gwamnan, ya bayyana cewa masu sauya shekar sun yi zabi nagari tunda suka dawo APC.

Ya basu tabbacin cewa jam’iyyar zata tabbatar da adalci da gaskiya ga dukkan mambobinta a dukkan lokaci, ba tare da la’akari da lokacin da suka shigo jam’iyyar ba.

Ya sha alwashin cewa gwamnatin da Abiodun ke jagora ba za ta kunyata mambobin ba ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye shiryen da za su kawo amfani akan tattalin arzikin mutane.

Egbetokun ya bukaci masu biyayya ga jam’iyyar da su tsaya a kudurinsu kuma kada su shiga ayyukan da ke iya bata sunan jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya rushe shugabancin hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Shugaban masu sauya shekan, Cif Kolawole Akinyemi ya bayyana cewa sun yanke shawaran shiga jam’iyyar ne sakamako nasarorin da gwamnan ya samu a halin yanzu.

A tabbatar da gaskiyar gwamnan, inda ya sha alwashin cewa zasu hada hannu tare da shi domin ganin cigaban jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel