Gwamna Ganduje ya taya Buhari murnar nasarar da yayi a kotun zabe

Gwamna Ganduje ya taya Buhari murnar nasarar da yayi a kotun zabe

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu a kotun karan zaben shugaban kasa.

Sakon ya zo ne a wani jawabin dauke da sa hannun babban sakataren labarain gwamnan, Malam Abba Anwar, inda ya kuma gabatar dashi ga manema labarai a Kano.

Yace: “Hukuncin ya kasance hujjar cewa an bi dukkan tsare-tsare da kuma hanyoyin da suka dace a lokacin da aka gudanar da zaben wanda babban jam'iyyar adawa da dan takararta ke kalubalanta."

Ya bayyana cewa Shugaban kasar ya jajirce domin ganin ya cigaba da gudanar da kyawawan ayyukan da ya fara a mulkinsa na farko daga 2015 zuwa 2019.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya rushe shugabancin hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Idan za ku tuna, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ita kanta jam'iyyar adawar sun shigar da kara kotun zabe a Abuja inda suka bukaci a soke nasarar da Buhari ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Febrairu 2018.

A lokacin da yake yanke hukunci akan lamarain, Justis Mohammed Garba yayi watsi da dukkan korafe korafen dake cikin rubutacciyar karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel