Wata tankar man fetur ta kife a kan hanyar dake tsakanin Enugu-Abakaliki

Wata tankar man fetur ta kife a kan hanyar dake tsakanin Enugu-Abakaliki

Wata motar tanka wadda take dauke da lita 33,000 na man fetur ta kife a kan hanyar Obinagu-Emene-Abakaliki dake karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar Enugun.

A lokacin kawo maku wannan rahoton ba a san hakikanin musabbabin faduwar wannan mota ba, amma sai dai jama’ar da ke bin hanyar akai-akai sun ce hatsarin bai rasa nasaba da ramukan da suka cika titin.

KU KARANTA:Dan sanda ya kashe wani dan-acaba a jihar Jigawa

Matafiya dake cikin kananan motoci sun ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 2:45 na yammacin Juma’a amma kuma babu wanda ya jikkata a sanadiyyar hatsarin.

A bangare guda kuwa, hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar Enugu, ta yi kira ga matafiya masu shiga ko fita daga jihar da su sauya hanya kafin a janye motar daga bisa hanyar.

Mrs. Nkechi Eneh, Sakatariyar hukumar ce ta bada wannan sanarwa, inda ta hada da gargadin al’umma mazauna wurin da motar ta fadi da su guji zuwa wurin motar da sunan diban man dake cikinta.

Majiyar jaridar Punch ta ruwaito cewa, a daidai lokacin da wakilinsu ya isa wannan wuri ya tarar da jami’an kwana-kwana da na NSCDC da kuma wasu hukumomin dake lura da irin wannan matsala idan har an samu aukuwarta.

https://punchng.com/fuel-tanker-falls-along-enugu-abakaliki-expressway/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel