Kotu ta bayar da belin Nazir Sarkin Wakan Sarkin Kano a kan N500,000

Kotu ta bayar da belin Nazir Sarkin Wakan Sarkin Kano a kan N500,000

- Kotu ta bada belin Nazir Ahmad, Sarkin wakan sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a kan N500,000

- Idan zamu tuna, 'yan sandan jihar sun kama mawakin inda kuma suka mikasa ga kotu

- Ana zargin gwamnatin da kamasa ne sakamakon wakokin batanci da yayi akan gwamnan Jihar

An sako Nazir Ahmad, Sarkin wakan Sarkin Kano, wanda aka kama sakamakon zarginsa da ake da sakin faya-fayan wakokinsa har biyu ba tare da izini ba.

Wata kotun majistare da ke Rijiyar Zaki a garin Kano ce ta bada belinsa akan N500,000.

Idan zamu tuna, an kama Sarkin wakan ne a ranar Laraba.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kamasa.

Yace an kama mawakin ne bayan umarnin da kotu ta bada.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

Kamar yadda yace: "Kotu ta bada damar kamasa kuma mun ni umarnin tare da mikasa ga kotu."

Ahmad ya shiga sahun mawaka irinsu Sunusi Oscar, Sadiq Zazzabi, Mohammed Yusuf AGY wadanda aka kama har aka turasu gidan maza sakamakon zarginsu da akai da cin mutuncin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Majiyarmu tace 'yan sanda sun tsinkayi gidan mawakin ne a yammacin Laraba bayan da suka samu damar bincike gidansa ko zasu samu wajen buga waka ba bisa ka'ida ba.

"Dama dai gwamnatin jihar na neman yadda zata kama Sarkin waka tun bayan da ya kalubalanci Ganduje a lokacin yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar."

"Ko bayan da aka gama duba gidansa, ba a samu wajen buga waka ba amma jami'an tsaro sunyi gaba da wasu faya-fayai daga gidansa," inji wata majiya da ta bukaci a boye sunanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel