Gwamna Masari ya rushe shugabancin hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Gwamna Masari ya rushe shugabancin hukumar jin dadin alhazai na jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya rushe shugabancin hukumar jin dadin alhazai na jihar wanda zai fara tasiri ba tare da bata lokaci ba.

Sakamakon haka, daraktan hukumar, Abu Rimi zai mika shugabanci ga babban darakta wanda zai ci gaba da jagorancin al’amuran hukumar har zuwa lokacin da za a yi sabbin nade-nade.

A wani jawabi daga babban hadimin mataimakin gwamnan akan harkokin labarai, Ibrahim Kalla, yace gwamnan ya yi godiya akan gudunmawarsu sannan yana musu fatan alkhairi a harkokinsu na gaba.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Mai alfarma sarkin Saudiyya, Sarki Salman, ya bayar da umurnin soke dokar biyan karin Riyal 2000 wanda yayi daidai da Naira 193,557 ga masu niyyar aikata aikin Umrah fiye da sau daya cikin shekaru biyu a jere.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sandan Sokoto ta nemi gwamnatin jihar ta haramta Shi’a kamar yadda aka yi a Kaduna

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya, NAHCON, ta bayyana hakan ne da safiyar Litinin, 9 ga watan Muharram 1441AH, wanda yayi daidai da 9 ga watan Satumba, 2019.

A shekarun baya, hukumomin kasar Saudiya sun kakaba dokar haraji na Riyal 2000 kan duk wanda ya ke son gudanar da aikin Umrah sau biyu ko fiye da haka a kasa da shekaru biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel