Rundunar yan sandan Sokoto ta nemi gwamnatin jihar ta haramta Shi’a kamar yadda aka yi a Kaduna

Rundunar yan sandan Sokoto ta nemi gwamnatin jihar ta haramta Shi’a kamar yadda aka yi a Kaduna

Kwamishinan yan sandan jihar Sokoto, Ibrahim Kaoje ya shawarci gwamnatin jihar da ta kafa dokar da zai haramta ayyukan yan Shi’a a cikinta kamar yanda aka yi a jihar Kaduna.

Ya bayar da shawaran ne yayinda yake jawabi ga manema labarai akan kama mambobin kungiyar guda takwas da aka yi, tare da wasu wadanda suka kwace bindigar Ak47 daga hannun dan sanda yayinda suke gudanar da tattakin Ashura a karamar hukumar Illela da ke jihar.

Kaoje ya bayyana cewa mutanensa sunyi nasarar kwato bindigar amman har yanzu mujallarsa na tare da su sannan cewa suna kokarin ganin sun kwato shi shima.

Rundunan Yan sandan har ila yau ta kama yan fashi Baito Na’alti na kauyen Dalijan, Kebbe da mambobin kungiyansa bayan korafe korafe da aka yi akansu.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: An tambayi masu neman aikin dan sanda sunan Shugaban kasa da na Shugaban alkalai basu sani ba

A wani lamari makamancin haka, rundunar ta kama Kabiru Bello na kauyen Manmande a karamar hukumar Gwadabawa da ke Sokoto bayan ya tanadi wuka, ya dauki hayar wani dan acaba Aliyu Usman daga yankin Kofar Kware a Sokoto (Wanda marigayi ne a yanzu) daga fadar Sultan zuwa Nakasarin Barebari.

Yayin da suke cikin tafiya ne ya caka mishi wuka a wuya sannan ya tafi da mashin din marigayin mai lamba TWB 38UQ.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel