Jan namiji: Wani dan acaba ya ceto wata budurwa da sojoji suka yi kokarin yi mata fyade

Jan namiji: Wani dan acaba ya ceto wata budurwa da sojoji suka yi kokarin yi mata fyade

- Wani dan acaba ya ceto wata budurwa da wani jami'in soja yayi kokarin yiwa fyade a jihar Legas

- Budurwar ta wallafa wani rubutu ne a shafinta na Twitter inda take godiya ga dan acabar da ya ceto ta

- Ta bayyana cewa sojan yayi kokarin yi mata fyaden ne bayan ya ganta da kaya irin na sojoji a jikinta

Wata mata ta wallafa wani labari a shafinta na Twitter, inda take godiya ga wani dan acaba da ya kai mata dauki a lokacin da wasu sojoji ke kokarin yi mata fyade bayan sun kamata sanye da irin kayansu.

Matar wacce ta sanya sunanta da @mideice, ta bayyana cewa sojojin sun kamata a Bus Stop na CMS dake jihar Legas, inda shi kuma dan acabar ya kai mata dauki, Sojan da ya dauke ta akan babur nashi bai bayyana mata inda zai kaita ba kawai taga ya shiga wani waje da ita mai duhu ne, inda yayi kokarin yi mata fyade.

KU KARANTA: Hankalin mutane ya tashi yayin da suka yi arba da macizai 43 a cikin jirgin sama a lokacin da yake tsakar tafiya

Dan acaban da ya dauko budurwar da farko ya bi bayan sojan da ya dauketa din, inda ya shiga har wajen da suka shiga, inda ya dauketa ya gudu da ita.

Ana ta samun karuwar laifuka na fyade a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel