Wata sabuwa: Da kama-kama aka shiga da Dino Melaye cikin kotu bayan yace ba zai iya tsayawa a cigaba da shari'ar shi ba

Wata sabuwa: Da kama-kama aka shiga da Dino Melaye cikin kotu bayan yace ba zai iya tsayawa a cigaba da shari'ar shi ba

- Dakyar aka shiga da Dino Melaye cikin kotu bayan ya bayyana cewa bashi da lafiya

- Hakan yasa kotu ta sake daga sauraron karar shi har zuwa ranar 3 ga watan Oktoba

- Sanatan ya dai ji ciwo ne a lokacin zaben fidda gwani na gwamnoni da aka yi a jihar Kogi lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wajen

Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya bayyanawa wata babbar kotu dake Abuja a jiya Alhamis 12 ga watan Satumba cewa yaji ciwo saboda haka ba zai iya tsayawa a cigaba da shari'a a kanshi ba.

Ana tuhumar Sanatan da laifuka guda shida ne wadanda suka hada da kokarin kashe kanshi, guduwa daga wajen jami'an tsaro, bata kayan 'yan sanda, da dai sauransu.

An gabatar da shari'ar shi a ranar 28 ga watan Mayun shekarar nan, sannan aka kara daga karar zuwa 11 ga wannan watan da kuma 3 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraron karar tashi.

KU KARANTA: Hankalin mutane ya tashi yayin da suka yi arba da macizai 43 a cikin jirgin sama a lokacin da yake tsakar tafiya

Sai dai kuma sai da wasu na kusa dashi suka taimaka mishi suka shiga dashi zuwa dakin shari'ar, inda ya bayyana cewa ba zai iya tafiya ba.

Daya daga cikin lauyoyin Dino ya bayyanawa kotu cewa Sanatan ya samu rauni a wajen zaben fidda gwani da jam'iyyar PDP tayi na gwamnoni a satin da ya gabata, a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wajen zaben.

Alkalin kotun ya karbi uzurin Sanatan, inda ya daga sauraron shari'ar zuwa ranar 3 ga watan Oktoba, domin cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel