Hankalin mutane ya tashi yayin da suka yi arba da macizai 43 a cikin jirgin sama a lokacin da yake tsakar tafiya

Hankalin mutane ya tashi yayin da suka yi arba da macizai 43 a cikin jirgin sama a lokacin da yake tsakar tafiya

- An kama wani mutumi da ya shiga da macizai masu cutarwa cikin jirgi

- Mutumin ya bayyana cewa yana so ya shiga dasu kasar Jamus ne domin sayar da su a can

- An kama mutumin a karshe bayan an zarge shi da karya dokar kasar Austria wajen shigo da dabbobi masu cutarwa

An sama macizai masu cutarwa guda 43 a cikin wani jirgin sama da zai je kasar Austria. Wani mutumi dan kasar Austria ne ya shiga dasu cikin jirgin wanda ya dauko su daga kasar Philippine.

Jami'an hukumar kwastam ne suka dakatar da mutumin a filin jirgin sama na Vienna, a cewar ma'aikatar kudi ta kasar Austria, kamar yadda jaridar Guardian ruwaito.

A lokacin da mutumin dan kasar Austrian ya isa garin Doha, jami'an tsaron sun tsayar dashi sun bincika jakarshi inda suka samu jakar cike da dabbobi masu cutarwa ga dan adam.

Da mutumin ya bayyana musu cewa akwai macizai masu cutarwa, ma'aikatan sun yanke hukuncin kai dabbobin gidan Zoo na Schoenbrunn, inda ma'aikatan wajen suka bude jakar.

KU KARANTA: Tsananin bakin ciki yasa tsohuwa 'yar shekara 63 fadawa rijiya, bayan wani limami yayi mata fyade

Mutumin ya bayyana cewa yana so ya shiga da dabbobin zuwa kasar Jamus ne domin sayar da su a can.

A karshe an garkame mutumin inda ake tuhumarsa da karya dokar kasar Austria ta kasuwanci wajen shigo da dabbobi masu cutarwa.

Gidan Zoo na Vienna, da kuma wani gidan Zoo a kasar ta Austria sun yarda su karbi dabbobin domin cigaba da kula dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel