Tsananin bakin ciki yasa tsohuwa 'yar shekara 63 fadawa rijiya, bayan wani limami yayi mata fyade

Tsananin bakin ciki yasa tsohuwa 'yar shekara 63 fadawa rijiya, bayan wani limami yayi mata fyade

- Wata mata tayi kokarin kashe kanta, bayan wani fasto yayi mata fyade

- Matar ta daka tsalle ne ta fada rijiya, sai dai kuma bata mutu ba, inda aka dauko ta

- Matar tace bakin ciki da bacin raine yasa take neman kashe kan nata, saboda fyaden da faston yayi mata

Wata mata 'yar kasar Zimbabwe mai shekaru 63 ta daka tsalle ta fada rijiya a kokarin da take na kashe kanta, bayan an zarge ta da wani Fasto yayi mata fyade.

A rahoton da jaridar Newsday ta ruwaito cewa, Wallas Pangenyama wanda yake a Mt Pleasant ya yiwa wata tsohuwa wacce aka boye sunanta, wacce bata jima da fara zuwa cocin ta shi ba.

Da take bayyana abinda ya faru a gaban kotun, matar ta bayyana cewa tayi kokarin kashe kanta saboda irin bacin rai da bakin ciki da take fama dashi.

An bayyana cewa a watan Maris din shekarar da ta gabata, Pangenyama dashi da wasu mambobin cocin shi sun kai ziyara garin Chivhu inda suka yi wa'azi, a lokacin ne matar ta shiga addinin nasu ita da sauran wasu mata.

KU KARANTA: Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna

Bayan sun koma addinin nashi, Pangenyama ya gayyaci matar da sauran matan da take tare dasu kai masa ziyara cocin shi, inda da suka je aka basu dakin da zasu kwana.

An ruwaito cewa safe, matar ta tashi ta shiga bandaki domin biyan bukatar ta, tana cikin bandakin sai Pangenyama ya shiga cikin bandakin shima, inda yayi mata fyade.

Bayan haka ta faru matar ta koma kauyensu inda ta sanarwa da mijinta abinda ya faru, shi kuma mijin ya nemi da taje ta kai kara wajen 'yan sanda.

An kama Pangenyama ne bayan matar ta kai karar shi ofishin 'yan sanda dake Harare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel