Magoya bayan fitaccen sanatan PDP fiye da 1000 sun koma APC

Magoya bayan fitaccen sanatan PDP fiye da 1000 sun koma APC

Mambobin jam'iyyar Peoples Demorcatic Party (PDP) masu goyon bayan Sanata Buruji Kashamu mai wakiltan Ogun East kimanin 1000 ne a ranar Juma'a suka dunguma suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Daily Trust ta ruwaito cewa mai bawa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin siyasa, Mista Tunji Egbetokun na ya tarbi masu sauya shekan a Abeokuta. Sun koma jam'iyyar na APC ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Dapo Abiodun.

Wakilin gwamnan, Mista Egbetokun ya ce wadanda suka koma jam'iyyar sunyi zabi mai kyau da suka dawo jam'iyyar 'masu son cigaba'.

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Ya basu tabbacin cewa ba za a nuna musu banbanci ba domin dukkan 'yan'yan jam'iyyar tsintsiya madaurin ki daya suke.

"Jam'iyyar mu tana maraba da kowa har 'yan wasu jam'iyyar. Kun zo a lokacin da ya dace. A jam'iyyar mu ba a nuna banbanci muna girmama kowa ba tare da la'akari da dadewa mutum a jam'iyya ba," inji shi.

Ya yi alkawarin cewa gwamnatin Abiodun ba za ta basu kunya ba wurin samar da tsare-tsare masu amfani da inganta rayuwar al'ummar jihar.

Egbetokun ya shawarci 'yan jam'iyyar su kasance masu dabi'u na gari kuma su guji aikata duk wani abu da zai bata wa jam'iyyar suna.

Sakataren jam'iyyar, Mr Ayo Olubori ya yabawa sabbin mambobin jam'iyyar saboda niyyar da suke da shi na bayar da gundunmawarsu wurin gina jihar.

Ya bukaci su gayyata sabbin mutane zuwa jam'iyyar domin su taru su ciyar da jihar gaba.

Shugaban masu sauya shekan, Cif Kolawole Akinyemi ya ce sun cimma matsayar shiga jam'iyyar ta APC ne saboda irin nasarorin da gwamnan jihar ya samu kawo yanzu.

Ya ce ya gamsu da tsarin gwamnan inda ya yi alakawarin cewa za su hada hannu tare domin su ciyar da jihar gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel