Manufar Buhari game da Najeriya ta bambanta da ta Osinbajo – Shehu Sani

Manufar Buhari game da Najeriya ta bambanta da ta Osinbajo – Shehu Sani

Tsohon sanata kuma fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil’adama a Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo na da banbancin manufa game da Najeriya.

Wannan zancen na Shehu Sanin a zuwa ne bayan da Shugaba Buhari ya ce mutum miliyan 100 za su fitar daga cikin halin talauci a shekara goma, yayin da shi kuma Osinbajo ya fadi cewa mutum miliyan 10 ne za a fitar a cikin shekaru goma.

KU KARANTA:Da zafinsa: Buhari ya fadi hakikanin abinda ya dauke hankalinsa daga damuwa a kan shari’arsa da Atiku

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan magana, tsohon sanatan ya ce akwai rudani tattare da jagorancin Najeriya ganin cewa kalaman shugaban kasa da mataimakinsa na cin karo da juna.

A wani labari makamancin wannan zaku ji cewa, Shugaba Buhari ya bayyana abinda ya hana jininsa hawa dangane da shari’arsa da Atiku.

Shugaban kasan ya ce taron majalisar zartarwa wato FEC wanda ya ci karo da lokacin shari’ar yayi matukar taimaka masa ta hanyar dauke hankalinsa daga shari’ar.

Buhari ya fadin wannan maganar ne fadar Villa ranar Juma’a 13 ga watan Satumba lokacin da gwamnonin APC suka kai masa wata ziyara ta musamman.

https://twitter.com/ShehuSani/status/1172478324851036165?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1172478324851036165&ref_url=https%3A%2F%2Fwww.informationng.com%2F2019%2F09%2Fbuhari-osinbajo-have-different-visions-for-nigeria-shehu-sani.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel