An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta nada Seun Onigbinde a matsayin mai bayar da shawara a Ma'aikatar Kasafin Kudi da tsare-tsaren kasa.

Onigbinde shine direkta kuma daya daga cikin wadanda suka kafa BudgIT kamfanin tattara bayanai da bincike da kuma bibiyar ayyukan gwamnatoci tare da wallafa bayannan ta a shafukan sada zumunta da jaridu.

BudgIT tana sukar wasu manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da mukarrabansa.

Bayan nadinsa, Onigbinde ya sanar da cewa zai rufe shafinsa na Twitter domin ya samu damar mayar da hankali kan sabon aikinsa.

DUBA WANNAN: Tinubu ya zayyana dalilai 9 da suka sa Buhari ya lallasa Atiku a kotu

Ga abinda ya rubuta.

"Abokai, na karbi wani aiki a matsayin mai bayar da shawara da wata cibiyar cigaban kasa da kasa ta bani na watanni shida. Domin kare kima da mutuncin BudgIT, ya dace in ajiye aiki kuma in sanar da sabon aikin da zan fara."

"A matsayin mai bayar da shawara, zan rika tallafawa karamin Ministan Kasafin Kudi da tsare-tsaren kasa, Prince Clem Agba wurin harkokin sauye-sauye na kasafin kudi, ayyukan cigaban kasa da inganta samar da kudin shiga.

"Wannan sabon matsayin ba shi da banbanci da irin wanda abokin mu kayi tare da abokin aiki na Joseph Agunbiade a 2013 - 2014 karkashin shirin DFID-FEPAR a ofishin Tsara Kasafin Kudi na Kasa da Nazari."

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan nadin, wasu na ganin dama yana sukar tsare-tsaren gwamnati ne don a bashi mukami yayin da wasu suke ganin yana da muhimmiyar rawar da zai iya takawa a gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel