Ba zan sake yin zanga zanga a Najeriya ba – Inji wani babban dan adawan Buhari

Ba zan sake yin zanga zanga a Najeriya ba – Inji wani babban dan adawan Buhari

Wani babban dan adawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Charles Oputa Charly Boy ya bayyana cewa daga yau ba zai sake shiryawa ko kasancewa cikin duk wani zanga zanga a Najeriya ba, sakamakon baya razana shuwagabannin Najeriya.

Charly ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin laabru a Abuja a ranar Juma’a, inda yace ya daina zanga zanga, kuma yana kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dasu nemi wasu hanyoyin tattaunawa da gwamnati, amma banda zanga zanga.

KU KARANTA: Zaben jahar Kogi: Sanata Dino Melaye ya yi watsi da tayin mukami da PDP ta yi masa

A cewarsa: “shuwagabanni basa tsoron zanga zanga, don haka basu nuna damuwa idan an yi zanga zanga, na kwashe tsawon shekaru 40 ina jagorantar zanga zanga a Najeriya, ina tabbatar muku da cewa zanga zanga ba zai canza halayen shuwagabanninmu ba.

“Mahaifina ya sha fada min a duk lokacin da naga zalunci na yakeshi saboda wata rana kaina zai dawo, kuma wannan shine dalilin da yasa n adage kai da fata wajen yaki da zalunci, Sojoji da Yansanda sun sha dukana saboda na fada ma gwamnati gaskiya.” Inji shi.

Daga karshe Charly dan shekara 68 ya bayyana cewa a yanzu zai koma tsohuwar sana’arsa ta waka don ya cigaba da wayar da kawunan yan Najeriya game da hakkokinsu tare da kira a garesu da su shiga cikin lamarin gina sabuwar Najeriya.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gaggauta kammala yarjejeniya tsakanin bangaren gwamnati da bangaren hadaddiyar kungiyar kwadago game da sabon karancin albashi domin fara biyan sabon albashin na N30,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel