Hukuncin kotu: Kawai ka rungumi kaddara - IPOB ta baiwa Atiku shawara

Hukuncin kotu: Kawai ka rungumi kaddara - IPOB ta baiwa Atiku shawara

A ranar Alhamis, Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo, ta baiwa dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, shawara.

Matasan sun shawarci tsohon mataimakin shugaban kasan cewa kawai ya rungumi kaddara ya hakura saboda nasarar shugaba Buhari ce hanya mafi tsauki ga zaman dan kabilar Igbo shugaban kasa a 2023.

Shugaban matasan Ohanaeze Ndigbo na kasa, Mazi okechukwu Isiguzoro, ya bayyana hakan ne yayin taya shugaba Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu kan Atiku Abubakar a kotun zabe ranar Laraba.

Yace: "Mun amince da nasarar shugaba Buhari saboda ita ce hanya mafi sauki ga shugabancin kasar Igbo a 2023."

KU KARANTA: Kungiyoyin fafutuka sun yi kira ga Buhari ya rufe tashar jirgin kasar Abuja/Kaduna

Bayan kwashe akalla sa'o'i takwas ana zaman kotu kan shari'ar dake tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP, shugaban kwamitin Alkalan kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar da PDP da Atiku suka shigar.

Alkalin ya bayyana hakan ne bayan yanke hukunci daya bayan daya kan zarge-zargen da Atiku da PDP sukayi kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari na cewa:

1. Bai cancanci takarar zabe ba saboda bai da takardan shaidan halartan makarantan sakandare

2. An yi amfani da Sojoji da yan sanda wajen magudi zaben

3. Kuri'un da hukumar INEC ta sanar ba kai yawan wanda ke shafin yanar gizonsu

4. An ci mutuncin yan jam'iyyar PDP a jihohi 11 lokacin zabe, da sauransu

5. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinajo, ya yi amfani da shirin Tradermoni wajen sayen kuri'u

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel