Da zafinsa: Buhari ya fadi hakikanin abinda ya dauke hankalinsa daga damuwa a kan shari’arsa da Atiku

Da zafinsa: Buhari ya fadi hakikanin abinda ya dauke hankalinsa daga damuwa a kan shari’arsa da Atiku

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakikanin abinda ya dauke hankalinsa daga kan shari’ar da aka gudanar tsakaninsa da Atiku Abubakar a kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ranar Laraba 11 ga watan Satumba.

Ganawar farko ta majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya wato FEC ta zo a daidai lokacin da ake fafatawa a kotu tsakanin Shugaba Buhari da Atiku Abubakar, inda PDP da Atiku ke kalubalantar nasarar Shugaba Buhari a zaben 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA:Gwamnatin Buhari ta shimfida tsari na musamman domin cigaban Najeriya – Sakataren gwamnatin tarayya

Kotun zaben ta tabbatar da nasarar Buhari ta hanyar yin watsi da korafin Atiku da jam’iyyarsa ta PDP. A cikin martaninsa dangane da shari’ar, Buhari ya ce: “Ban damu sosai ba game da shari’ar saboda na san cewa mu ‘yan Najeriya suka bai wa kuri’unsu. Kwatsam kuma sai gashi gaskiya tayi halinta.”

Amma kuma Shugaba Buhari ya sake fadin wata magana ta daban a lokacin da ya karbi bakwancin gwamnonin APC ranar Juma’a a fadarsa ta Villa, inda ya ce taron FEC ne ya dauke hankalinsa daga abubuwan dake gudana a kotun.

“A wannan ranar da ake gudanar da shari’a sai abin ya ci karo da taron FEC. Na godewa Allah da wannan al’amari saboda taron majalisar zartarwar ya dauke hankalina daga kan shari’ar kotun.

“Mun dauki tsawon sa’o’i bakwai muna tattaunawa yayin da su kuwa a can kotun suka dauki tsawon awa tara ana gudanar da shari’a. Da ba dan wannan tattaunawar ta yiwu in samu rashin natsuwa da kwanciyar hankali.

“Amma na godewa Allah da ya sanya abin ya zo a haka ba tare da jinina ya hau ba ko kuma wani abu mai kama da wannan ya sameni. Ina godiya a gareku a sakamakon tayamu murna da kuka yi.” Inji Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel