Zamu kawo karshen rikicin manoma da makiyaya – NSCDC

Zamu kawo karshen rikicin manoma da makiyaya – NSCDC

Kwamandan hukumar tsaron farar hula ta Najeriya wato NSCDC reshen jihar Jigawa, Alhaji Garba Muhammad ya ce a shirye suke domin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma ta hanyar amfani da sabon tsarin jami’ai masu shiga gona na hukumar.

Muhammad wanda ya fadi wannan maganar a lokacin da ya ziyarci shugaban karamar hukumar Mallammadori, Alhaji Hussaini Umar ranar Juma’a ya ce aikin jami’an dai shi ne yaki da masu garkuwa da mutane, da kuma rikicin makiyaya da manoma.

KU KARANTA:Da zafinsa: Buhari ya fadi hakikanin abinda ya dauke hankalinsa daga damuwa a kan shari’arsa da Atiku

A cewarsa, a karkashin rundunarsa an dauki jami’ai 30 inda aka ba su horo na musamman a makarantar horror da jami’an NSCDC dake jihar Katsina.

Ya kuma kara da cewa, sauran jami’an za su samu na su horon ne a cikin rukunnai daban-daban. Kwamandan ya shaidawa shugaban karamar hukumar dalilin ziyarar tasa inda ya ce goyon bayansu yake neman domin samun nasara bisa abinda ke gabansu.

Umar Hussaini wanda mataimakinsa, Idris Abdullahi ya wakilta ya bayyana murnarsa dangane da ziyarar kwamandan NSCDC.

Ya kuma roki kwamandan hukumar cewa a kara wa karamar hukumar ta su yawan jami’an tsaron farar hula domin shawo kan yawan jama’a da yankin ke fama da shi. Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ne ya fito da wannan labarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel