Rashin tsaro: Kungiyoyin fafutuka sun yi kira ga Buhari ya rufe tashar jirgin kasar Abuja/Kaduna

Rashin tsaro: Kungiyoyin fafutuka sun yi kira ga Buhari ya rufe tashar jirgin kasar Abuja/Kaduna

Gamayyar kungiyoyin fafutuka a ranar Juma'a sun gudanar da zanga-zangan lumana a jihar Kaduna inda suke kira ga gwamnatin tarayya ta rufe tashar jirgin saman Kaduna/Abuja sakamakon yawaitan garkuwa da mutane kan hanyar mota.

Wanda ya shirya zanga-zangar, Yusuf Amoke, yayinda yake jawabi ga manema labarai ya ce idan aka kulle tashar jirgin kasar, manyan yan siyasa da manyan jami'an tsaro da ke amfani da jirgin zasu nemo mafita kan rashin tsaron hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce masu garkuwa da mutanen bayan tare hanya da sukeyi, sun fara shiga gidajen mutane suna garkuwa da su.

KU KARANTA: Dan Najeriya, Hafiz Idris Abubakar, ya lashe musabakar Al-Qur'ani na duniya

A cewarsa:"Yan ta'addan suna tare hanya lokacin da suka ga dama kuma suyi awon gaba da mutane cikin daji kuma su nemi kudin fansa daga baya daga wajen iyalansu ba tare da la'akari da talaucin da suke fama da shi ba."

"Wannan abu ya zama ruwan dare a hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma kowa kansa ya sani yanzu maimakon daukan mataki."

"Hakan ya sanya mutane sun gujewa bin titin. Jirgin kasan ya zama na masu uwa a gindin murhu ."

"Babban abin bakin cikin shine yanzu masu kudi ke hawa jirgin. Manyan jami'a gwamnati irinsu ministoci, sanatoci, shugabannin ma'aikatu, sun koma amfani da jirgin. Tambayar shien, zuwa yaushe za'a cigaba da hakan?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel