Tinubu ya zayyana dalilai 9 da suka sa Buhari ya lallasa Atiku a kotu

Tinubu ya zayyana dalilai 9 da suka sa Buhari ya lallasa Atiku a kotu

- Daga karshe Tinubu ya fadi dalilan da yasa Atiku da jam'iyyar PDP suka sha kaye a kotun zabe

- A ranar Laraba 11 ga watan Satumba ne kotun sauraron karar zaben shugaban kasa tayi watsi da karar da aka shigar na kallubalatantar nasarar Shugaba Buhari a zaben da ya gabata

- Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce Atiku ya dogara ta da cewa an tura sakamakon zabe zuwa wata matattara da musamman da babu ita

Jigo a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilan da yasa jam'iyyar PDP da dan takararta Atiku Abubakar suka sha kaye hannun Shugaba Buhari a kotun zaben shugaban kasa.

Legit.ng ta ruwaito cewa duk da cewa kotu ta bawa Atiku da jam'iyyarsa damar gabatar da hujja kan karar da suka shigar, tsohon mataimakin shugaban kasar ba shi da wata madogara kwakwara sai dai wata matattara wato server da babu ita.

Tinubu ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar 13 ga watan Satumba inda ya ce kotun ta bi dokokin kasa kuma ya yabawa dukkan bangarorin biyu saboda nuna dattaku.

Ga dai dalilan da jigon na APC ya ce sune suka sa Atiku da jam'iyyar PDP suka sha kaye.

1. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku da lauyoyinsa suna da ikon gabatar da hujojinsu a kotu. An bar su sun gabatar da hujojinsu ba tare da tsangawa ko barazana ba.

2. Babu wanda ya yi amfani da karfin mulki domin musguna musu. Kamar yadda kotu ta tabbatar an gudanar da zabe mai tsafta kuma an amince da sakamakon.

3. Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa Shugaba Buhari bai cancanta ya yi takara ba. Shugaban kasar bai tayar da hankalinsa kan wannan cin fuskan ba. Kotu daga karshe ta wanke shi.

4. Bisa la'akari da karatunsa da kwarewa da ya samu yayin ayyukan da ya yi a rayuwarsa, kotu ta zartar da cewa Shugaba Buhari ya cancanci tsayawa takara kuma bai aikata wani lafi ba yayin mika fom dinsa ga INEC.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa

5. Atiku kuma ya yi dogara da wata surkulle na cewa anyi amfani da card reader an tura sakamakon zabe zuwa wani matattara. Kotu ta gano cewa dokan zabe na yanzu bata bayar da damar yin hakan ba.

6. Atiku ya gaza gabatar da hujojjin cewa an tura sakamakon zabe zuwa matattara. Hasali ma hakan ba zai iya yiwuwa ba. Ba a kera card reader domin wannan aikin ba kawai dai matattaran da suke zance surkulle ce.

7. A bangarensu, lauyoyin Atiku sun yi kokari wurin gabatar da hujojinsu amma daga karshe dai duk abinda su kayi ikirari ba hakan su ke ba. Kawai suna fadin abinda suke mafarkin ganin ya faru ne.

8. Ita kuma kotu tana aiki ne kawai da hujja ba shaci fadi ba. Kotu ta gano cewa an yi zabe cikin inganci kuma Shugaba Buhari ya lashe zaben ta tazara mai yawa kamar yadda INEC ta sanar.

9. An bawa Atiku damar ya gabatar da hujojinsa amma daga karshe ya gaza yin hakan. Ba kuma wai don bai yi kokarin kare hujojinsa bane sai dai saboda babu hujojin ne. Shugaba Buhari ya lashe zabe ba tare da wata kumbiya-kumnbiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel