Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa tare da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Tuni dai gwamnonin sun samu wajen zama bayan sun isa fadar shugaban kasa domin fara ganawar.

Jaridar Vaguard ta ruwaito cewa daga cikin wadannda suka hallara harda Atiku Bagudu na jihar Kebbi wanda shine Shugaban kungiyar gwamnonin APC.

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Asali: Facebook

Sauran sun hada da Gboyega Oyetola na jihar Osun, Mohammed Inuwa na jihar Gombe, Abdulrazak Abdulrahman na jihar Kwara, Abdullahi Ganduje na jihar Kano

Har ila yau Simon Lalong na jihar Plateau wanda shine kuma Shugaban kungiyar gwamnonin arewa ma ya hallara.

Ga hotunan ganawar a kasa:

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Asali: Facebook

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Asali: Facebook

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Wani dan shekara 35 ya shiga tasku kan kashe wani dan achaba a Katsina

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa uku sun yi wata ganawa a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka gana da Shugaban kasar sun hada da ministan jiragen sama, Hadi Sirika; Minsitan Niger Delta, Godswill Akpabio; da kuma ministan kimiyya da fasaha, Ogbonanya Onu.

Buhari ya fara ganawar da ministocin daya bayan daya, inda ya fara da Sirika, sannan Akpabio, sai kuma Onu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel