Gwamnatin Buhari ta shimfida tsari na musamman domin cigaban Najeriya – Sakataren gwamnatin tarayya

Gwamnatin Buhari ta shimfida tsari na musamman domin cigaban Najeriya – Sakataren gwamnatin tarayya

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shimfida wani tsari na musamman domin samarwa kasar Najeriya cigaba a fannin tattalin arziki, noma, lantarki, sufuri da kuma kere-kere.

Mustapha ya fadi wannan maganar tasa ne a jiya Alhamis 12 ga watan Satumba a yayin wata liyafa ta godiya da murna sakamakon nasarar Shugaba Buhari a kotun zabe ranar Laraba.

KU KARANTA:Kar kuyi gaggawa wurin neman tara dukiya, sakon Magu ga ‘yan Najeriya

Ya ce, gwamnatin Buhari ta gudunar da jagoranci cikin taka-tsan-tsan da kuma amana a dukkanin matakai tun lokacin hawansa.

Boss ya kara da cewa: “Akwai nasara a bangaren yaki da Boko haram, hare-harensu sun rage a yanzu sabanin yadda suke yi a shekarun baya. Wannan shi ke nuna maku cewa gwamnatin Buhari da gaske ta ke wurin yaki da matsalolin tsaro.

“Baya ga Boko haram ana cigaba kokarin fada da sauran matsalolin tsaron kasar nan wadanda suka shafi, garkuwa da mutane da kuma rikicin manoma da makiyaya.

“Yaki da cin-hanci na cigaba da gudana kamar yadda muka soma tun a wa’adin na farko. Matakan da muka dauka wurin hana sata sun taimaka kwarai wurin yin tattali da ajiyar biliyoyin kudi.” Inji sakataren.

A karshe sakataren gwamnatin tarayyar yayi kira ga ‘yan jarida da su guji yada labaran da ba su da tushe balle makama, inda ya ce gwamnati ba za ta hana kowa yin aikinsa ba amma dai ya kamata su gujewa yada labarai na karya.

https://www.dailytrust.com.ng/buhari-govt-has-laid-solid-foundation-sgf.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel