Nasarar Buhari a kotu: Wani dan PDP ya cakawa dan APC kwalba

Nasarar Buhari a kotu: Wani dan PDP ya cakawa dan APC kwalba

Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai goyon bayan jam'iyyar PDP, Best Uduophori ya cakawa wani magoyin bayan jam'iyyar APC, Elvis Omoiri kwalba saboda ya yi murnar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa wani da abin ya faru a gabansa ya ce Omoiri ya tafi zauren shan giya ne mallakar Uduophori a unguwar Okolona a Warri a ranar Alhamis kwana guda bayan yanke hukuncin domin ya yi murnar nasarar Buhari tare da abokansa amma wai sai mai wurin wanda mai goyon bayan jam'iyyar PDP ne ya caka masa kwalba.

Rikicin ya fara ne lokacin da Omoiri ya shigo wurin yana nuna farin cikinsa kan hukuncin da kotun ta zartar.

Amma shi Uduophori ya nuna kin amincewarsa da hukuncin da kotun ta yanke.

DUBA WANNAN: Gwamna Makinde ya nada 'yan jam'iyyun hamayya biyu a matsayin hadimansa

Lamarin ya yi wa Uduophori zafi hakan yasa fasa kwalba da caka wa mai goyon bayan jam'iyyar na APC.

Wanda abin ya faru a idonsa ya ce "Mashayar ta Uduophori tana kofar gidan su Omoiri ne kuma ba yau suka fara jayaya kan banbancin ra'ayin siyasa ba sai dai a yau lamarin ya kazanta inda har ya caka masa wuka kuma ya nemi hana a kai shi asibiti.

"Omoiri dan kabikar Isoko ne daga garin Ivrogbo-irri a karamar hukumar Isoko ta kudu na jihar delta kuma dan gani kashe nin gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ne."

A halin yanzu dai wanda aka caka wa wukan yana asibiti kuma ba zai iya magana ba saboda yana barci lokacin da Sahara Reporters suka tuntubi asibitin.

'Yan sandan da suka ziyarci asibitin domin daukan rahoto kan abinda ya faru suma ba su can uffan ba kan batun amma daya daga cikinsu da ya nemi a boye sunansa ya ce wannan lamarin yunkurin kisar gilla ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel