Shugaba Buhari, Akpabio, Sirika da Onu sun shiga labule

Shugaba Buhari, Akpabio, Sirika da Onu sun shiga labule

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa uku sun yi wata ganawa a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka gana da Shugaban kasar sun hada da ministan jiragen sama, Hadi Sirika; Minsitan Niger Delta, Godswill Akpabio; da kuma ministan kimiyya da fasaha, Ogbonanya Onu.

Buhari ya fara ganawar da ministocin daya bayan daya, inda ya farad a Sirika da misalign 11:30 na safe.

Sai ya kuma gana da Akpabio da karfe 12:00 na rana, yayinda Onu ya zo da misalign 12:30 na rana.

Da karfe 1:00 na rana, Sirika da Onu suka kammala ganawarsu da Shugaban kasar inda suka bar fadar Villa.

Akpabio kadai aka bari tare da shugabann kasar. Ba a san ajandar ganawar tasu ba.

KU KARANTA KUMA: Da zaran ka iya karatu, rubutu, da fahimta, toh kana iya tsayawa takarar zabe – Tanko Yakassai

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa babu mamaki sun zo ganin Shugaban kasar ne domin gabatar da wasu lamura da suka shafi aikinsu.

An tattaro cewa dukkaninsu sun bi ta hannun Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Mallam Abba Kyari, kamar yadda Buhari ya bukata a baya cewa duk ministan da ke son ganinsa ya bi ta ofishin Kyari domin ganinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel