A shirye muke don sake kayar da Atiku a kotun koli, inji Oshiomhole

A shirye muke don sake kayar da Atiku a kotun koli, inji Oshiomhole

- Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, yace a shirye suke don sake kada Atiku a kotun koli

- Oshiomhole yace a shirye yake don fuskantar Secondus, inda zai zo na biyu, shi kuwa yazo na farko

- Ya ba jam'iyyar hamayyar shawara akan ta bi sahun magoya baya don cigaban kasar nan

Jam'iyya mai mulki ta APC tace a shirye take don fuskantar PDP da Atiku Abubakar a kotun koli akan shari'ar zaben 2019.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa a Abuja.

Yace dalilan da suka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari nasara a kotun sauraron kararrakin zabe su zasu basa a kotun koli.

"Muna da kwarin guiwar cewa in dai a cikin dokokin Najeriya ne, toh PDP ta je har kotun duniya ma, zamu hadu. Kotun koli ta Najeriya ce ba ta PDP ko APC ba."

"A shirye muke, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye yake da kara maka Atiku da kasa a kotun. Kuma Adam Oshiomhole shirye yake don fuskantar Dan uwansa Secondus a kotu. Zai zo na biyu, ni kuma na farko," inji shi.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

Yace jam'iyyar PDP ta yaudari kanta da ta daukaka kara da tunanin Dan takararta zai yi nasara.

Shugaban jam'iyyar APC din ya hori Atiku Abubakar da sauran 'yan jam'iyyar PDP da su manta da abinda ya faru a yayin zabe. Su koma don goyon bayan shugaban kasa ko don cigaban kasar nan.

"An gama da matsalar, gara kowa ya koma bayan mai nasara don cigaba. Duk da cewa, mai nasararmu ne ya tabbatar mana da cewa faduwa a zabe ba shine karshen rayuwar siyasar mutum ba. Ya fadi sau 3 amma yau ga shi a shugaban kasa," inji shi.

Shugaban jam'iyyar APC yayi godiya ga ma'aikatar shari'a akan aikinta da tayi don tabbatar da dokokin zaben kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel