Wani dan shekara 35 ya shiga tasku kan kashe wani dan achaba a Katsina

Wani dan shekara 35 ya shiga tasku kan kashe wani dan achaba a Katsina

Wani dan shekara 35 mai suna Adamu Muhammed mazauni Area Quarters da ke yankin karamar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina, ya gurfana a gaban kotun Majistare da ke Katsina a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, bisa zargin kashe wani dan acaba mai suna Nura Mohammed.

An kama Adamu a ranar 23 ga watan Mayu, 2019, yayin da yake tukin babur din marigayi Mohammed jim kadan bayan kisan marigayin.

Yan sandan sun kama shi da laifuffuka uku na hadin baki, fashi da kuma kisa.

Laifuffukan sun saba ma sashi na 6, 1 da 2 (a) (b) na dokar fashi da makami, Cap II, LFN, 2004, da sashi na 221 na doka.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sajen Lawal Bello ya bukaci kotun da ta daga karan don ba rundunar yan sanda damar kammala binciken ta.

A cewar yan sandan, yan daba sun kashe marigayin sannan suka tafi da babur dinsa a hanyar Malumfashi/Da Konjiba a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Da zaran ka iya karatu, rubutu, da fahimta, toh kana iya tsayawa takarar zabe – Tanko Yakassai

Jaridar Punch ta rahoto cewa an kashe Marigayi Mohammed na Damfili Quarter, Malumfashi ne yayin da yake tukin babur dinsa wacce bai yi mata rijista ba.

Mai shari’a Hajiya Fadile Dikko, ta bukaci a cigaba da tsare mai laifin a kurkuku sannan ta daga karan zuwa ranar 16 ga watan Oktoba, 2019 don cigaba da saurara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel